Darajar Naira za ta ci gaba da farfadowa – Shettima

0
181

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shatima ya bayyana gamsuwarsa da yadda kudin naira ke ƙara samun daraja a kasuwannin canji, inda ya ce kudin naira za ta cigaba da farfadowa a kan dalar Amurka.

Shatima ya ce a bisa dole Shugaba Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur da hawansa mulki, tare da barin kasuwa ta yi halinta dangane da canjin kudaden waje, la’akari da yadda tsohon tsarin ke sa wasu tsiraru kudancewa a dare daya.

Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana haka ne yayin ganawa da tawagar ƙungiyar masu masana’antu da ‘yan kasuwa ta jihar legas a ofishinsa da ke birnin Abuja.

Sanata Shatima ya kuma ce dole a godewa Tinubu da irin tsarin mulki da gwamnatinsa ta zo da shi sannan ya tunatar da batun salon mulkin sa ya na gwamnan Legas, wanda a cewar shi, shi ne musabbabin cigaban da ake samu a jihar Legas yanzu haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here