Kotu ta kasa zama kan umarnin hana EFCC kama Yahaya Bello

0
87
Yahaya Bello

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya kasa sauraron karar da hukumar EFCC ta shigar kan umarnin hana kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

A ranar Litinin kotun daukaka karar da ke Abuja ta gaza zaman sauraron karar da EFCC ta shigar kan umarnin wata babbar kotun da ke Lokoja da ta hana hukumar damke Yahaya Bello.

A ranar 17 ga watan Afrilu kotun da ke Jihar Kogi ta ba da umarnin hana EFCC kama Yahaya Bello, tsare shi ko gurfanar da shi gaban kuliya.

A wancan lokaci da alƙalin, Alkalin, I.A Jamil, yake yanke hukunci, jami’an EFFCC ɗauke da umurnin wata babbar kotu a Abuja suka yi wa gidan Yahaya Bello da ke birnin kawanya, domib kama shi, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Hukumar EFCC, mai yaki da masu karya tattalin arziki, tana neman gurfanar da tsohon gwamnan ne bisa tuhume-tuhume 19 na badakalar kudi, zamba cikin aminci da cin amana da kuma karkatar Naira biliyan 80.2.

Hukumar ta lashi takobin ganin Yahaya Bello ya fuskanci shari’a kan laifukan da ake zargin sa.

A kan haka ne ta ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a wancan ranar domin samun izinin kama shi.

A lokacin ne Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin a gurfanar da tsohon gwamnan a gabansa a ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here