Wadansu yan bindiga na neman sulhu da mu – Ribadu

0
90
Ribadu

Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya ce akwai wadanda daga cikin ƴanbindigar da suka samu fahimtar juna da su: “Nasani wannan abin idan Allah zai kawo mana sauki sai mun samu fahimtar juna, domin wadanda suke yin wannan abun ƴan uwanmu ne masifa ce ta zo mana”.

Nuhu Ribadu ya ce suna ƙoƙarin samun fahimta tsakaninsu da wasu ƴanbindigar.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki, koda yake basa fitowa fili su bayyana matakan da suke dauka saboda yanayin aikin tsaro ba a magana.

Nuhu Ribadu ya ce akwai canje-canje da aka samu da dama musamman wajen adadin mutanen da ake kashewa a Najeriya kowane wata, inda lokacin da suka hau mulki ana kashe dubban mutane, “yanzu idan mutum ya je Neja Delta ya san an yi aiki, haka ƙasar Inyamurai, ofishin ƴansanda kusan 50 duk an tada su a baya amman yanzu duk sun koma suna aiki, kuma mun kawo ƙarshen zaman gida na dole da a baya ake yi a yankin, haka a yankin Arewa maso gabas an rage yawan kashe-kashe sosai”.

Mai ba shugaban Najeriyar shawara kan tsaro ya ce sun yi nasarar kashe wasu da dama daga cikin shugabannin ƴanbindiga da suka da Ali Kachallah wanda ya jagoranci harin jami’ar Gusau ta jihar Zamfara da aka sace dalibai da kuma Boderu da Damina da Dangote da sauransu.

Nuhu Ribadu ya ce an samu tsaro a ƙasar idan aka yi la’akari da yadda yanzu mutane ke zuwa duk inda suke so ba tare da fargaba ba.

Najeriya dai na fuskantar matsalar tsaro a kowane ɓangare na ƙasar, lamarin da hukumomi ke cewa sun kusa kawar da shi.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here