Ministan sufuri a Najeriya, Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana.
Hakan na zuwa ne kwana É—aya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga titin jirginsa a tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed da ke Legas.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan ya kuma umarci a gudanar da bincike kan kamfanin.
Binciken zai shafi dukkan matakan kariya da hanyoyin yin gyara domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin umarnin Æ™a’idojin tafiyar da harkar sufurin jirage.
Acikin wata sanarwa da aka aikewa darakta janar na NCAA, minsitan ya ce matakin ya zamo wajibi domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin Æ™a’idojin aiki musamman na matakan kariya.
Jirgin Dana É—auke da fasinja 83 da ya taso daga Abuja zuwa Legas ya zame daga kan titinsa ranar Talata.
I want to u a like me work buesesse, l. A. G. Dawakin kudu Yankatsari chiromawa