Fursunoni sama da 100 sun tsere daga gidan yarin Suleja

0
76

Hukumomi a Nijeriya sun ce fursunoni aƙalla 118 sun tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Neja bayan wani mamakon ruwan sama da ya rusa wani ɓangare na ginin gidan ranar Laraba.

“An tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na sa’o’i da dama ranar Laraba da daddare, lamarin da ya haddasa ɓarna a gidan gyara hali na Suleja da ke jihar Neja, da wasu gine-ginen da ke kewaye,” a cewar sanarwar da mataimakin babban jami’in hulda da jama’a na hukumar gidajen gyaran hali ta Abuja, AS Duza, ya fitar a ranar Alhamis. 

Sanarwar ta ƙara da cewa ”ruwan saman ya lalata wani ɓangare na gidan yarin, ciki har da katanga da ta kewaya ginin wanda ya ba da dama ga fursunoni 118 suka tsere”.

Sai dai ya ce an kama 10 daga cikin fursunonin da suka tsere kuma tuni aka mayar da su gidan gyara halin. 

“Cikin hanzari hukumar gidan yarin ta baza jami’anta tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro waɗanda kawo yanzu suka yi kamo mutum 10 daga cikin fursunonin da suka tsere, sannan muna ci gaba da ƙara ƙaimi wajen nemo sauran,” in ji shi.

Sanarwar ba ta yi cikakken bayani game da fursunonin da suka tsere ba amma a baya gwamnatin ƙasar ta tsare mayaƙan Boko Haram a gidan yarin Suleja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here