Karancin mai: Dogayen layukan mai ya dawo a wasu jihohin Najeriya

0
119

A baya-bayan nan ana wayar gari da ganin motoci sun kafa layi a gidajen mai yayin da wasu direbobi ke kokawa kan yadda farashin man ya tashi.

Binciken da jaridar Daily Trust ta yi a Abuja da Kano da Kaduna da Legas ya nuna cewa ana samun dogayen layukan mai a gidajen mai da dama.

A Abuja, babban birnin Najeriya, galibin gidajen man da ke ƙwaryar birnin ba su da man.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu manyan gidajen mai sun rufe ƙofa inda suka ce ba su da mai.

Sai dai a gidajen man NNPCL cikin ƙwaryar birnin, ana samun mai sai dai akwai dogayen layukan motoci.

Tsirarun gidajen mai da ke da man kuma sun ƙara kuɗi da ya kai N750 kowace lita daya.

A Kano ma direbobi na shafe tsawon sa’oi a gidajen mai kafin su samu man.

An fi ganin layukan man a gidajen mai na NNPC a da ke Kofar Nasarawa da ke kan titin Ibrahim Taiwo.

A jihar Kaduna ma, an ga layukan mai a gidajen da ke sayar da shi.

Haka batun yake a Legas inda NNPC ke sayar da N560 duk lita É—aya yayin da manyan dillalan mai ke sayar wa a kan N590 da N610.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here