Amurka na ganawa da gwamnatin Nijar kan janye dakarunta daga kasar

0
89

Amurka ta ce jami’anta na ganawa da sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa game da batun janye sojojinta daga Nijar ɗin.

Hakan ya zo sakamakon makonni da gamayyar ƙungiyar farar hula a Nijar ta shafe tana zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar ranar 26 ga watan Yuli.

“Jakadiyar Amurka a Nijar, Kathleen FitzGibbon da Manjo Janar Ken Ekman, Daraktan tsare-tsare da tattaunawa na rundunar tsaro ta Amurka da Afirka za su gana da mambobin Majalisar Tabbatar da Tsaron Ƙasa (CNSP) da ke Yamai,” in ji wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar.

A mako mai zuwa ne, wasu jami’an tsaron Amurka za su kai ziyara Yamai domin tsara yadda za a kwashe sojojin ƙasar cikin mutunci da gaskiya.

A cewar wata sanarwa, gwamnatin Amurka za ta ci gaba da goyon bayan al’ummar Nijar yayin da suke ƙoƙarin fatattakar mayaƙa.

Sanarwar ta kuma ce mataimakin sakataren harkokin waje, Kurt M. Campbell zai je Yamai a watanni masu zuwa domin tattauna batun yin haɗin gwiwa a batutuwan da buƙatarsu ta zo ɗaya.

Sojojin Nijar sun sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro da Amurka yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙaruwar matsalar tsaro da hare-hare daga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Magoya bayan gwamnatin sojoji a Nijar sun ce kasancewar sojoji har da na Amurka da Faransa ba ya tasiri ga tsaron ƙasar.

A yanzu, sojojin sun ƙulla yarjejeniya da Rasha, a wani mataki da zai faɗaɗa tasirin Moscwo a Afrika.

A makon da ya gabata ne, ƙwararrun sojojin Rasha suka isa Yamai domin horas da dakarun Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here