Mun shawo kan matsalar da ta jawo layuka a gidajen mai – NNPC

0
150

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya ce ya shawo kan matsalar da ta jawo dogayen layuka a gidajen mai da ke faɗin ƙasar. 

Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis, NNPCL ya ce an samu matsalar ne saboda “ɗawainiyar wajen jigilar man”. 

“NNPCL na tabbatar da cewa wahalar da ake sha wajen samun man fetur a wasu sassan Najeriya ta faru ne saboda matsalar da aka samu wajen jigilar man kuma yanzu an kawo ƙarshen ta,” in ji sanarwar. 

Kamfanin ya ƙara da cewa ba shi da niyyar sauya farashin man, wanda tuni ‘yan kasuwa suka ƙara farashinsa a jihohi. 

Lita ɗaya ta man ta zarta N750 a Abuja babban birnin ƙasar. 

Tun daga farkon makon nan aka fara ganin layuka a gidajen mai a Abuja, inda matsalar ta bazu zuwa jihohi daga baya.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here