Gwamnatin Kano ce ta dauki nauyin zanga-zangar adawa da ni – Ganduje

0
158
Ganduje

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyar NNPP da ke jagorantar gwamnatin Jihar Kano ce ke da hannu a zanga-zangar adawa da shi da aka gudanar a Abuja.

Sai dai tunin Gwamnatin Kanon ta musanta zargin cewa tana da hannu zanga-zangar adawa da Ganduje.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi zanga-zangar neman a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, inda ƙungiyoyi da jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta tsakiya ke kan gaba.

Gwamna Ganduje ya yi zargin ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta hannun mai taimaka masa na musamman kan ƙungiyoyin farar hula, Kwamared Okpokwu Ogenyi.

Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Kano na ɗaukar hayar masu zanga-zanga waɗanda galibi ‘yan Kwankwasiyya ne da suka fito daga yankin Arewa ta Tsakiya wajen neman da ya yi murabus.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Muna da sahihan bayanai cewa Gwamna Yusuf na aiki tare da wasu daga shiyyar Arewa ta Tsakiya tare da bayar da maƙudan kuɗaɗe ga wasu mutane domin ci gaba da neman sauya Ganduje tare da jagorantar kwamitin tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

“Yanzu sun koma yin amfani da wasu mutane a shiyyar Arewa ta Tsakiya domin neman a tsige Ganduje bayan sun kasa cimma matsaya na sa tsageru a Jihar Kano.

“Abin da ya dame mu shi ne yadda ake ɓarnatar da dukiyar ƙasa a Jihar Kano duk da buƙatar samar da ababen more rayuwa ga al’ummarmu. Wannan siyasa ce ta wuce gona da iri.”

Ganduje ta bakin Kwamared Okpokwu ya yi kira ga jami’an tsaro da su sanya ido domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

“Wasu daga cikin masu zanga-zangar da aka ɗauka hayar su ma sun manta cewa sun sa rigar Kwankwasiyya da hula a yayin zanga-zangar zuwa sakatariyar APC ta ƙasa, duk da haka ya yi iƙirarin cewa su ‘yan jam’iyyar APC ne; wannan mataki ne mai hatsarin gaske don daƙile zaman lafiyar jam’iyyarmu.”

Aminiya ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa sai dai bai amsa kiran da aka yi masa ba da saƙon tes da aka aika masa.

Sai dai a kwanakin baya Dawakin Tofa ya shaida wa Aminiya cewa Jam’iyyar NNPP da gwamna mai ci ba su da alaƙa da wani abu da ke faruwa a wajen jam’iyyarsu ta siyasa.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here