Nakiya ta hallaka mayakan sa kai 11 a Borno

0
125

Wasu mayakan sa kai guda 11 da ke yaki tare da sojojin Najeriya masu yakar yan ta’adda suka mutu a lokacin da motarsu ta taka nakiya a kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

Majiyar ta bayyana cewa mayakan jihadi dai na kara yin amfani da nakiyoyi a kan tituna a wannan yaki na sunkuru da suke yi da dakarun Najeriya wajen kai hare-hare kan fararen hula tun bayan da aka fatattaki su daga yankunan da suke iko da su a shekarun farko na tada kayar bayan da suka shafe shekaru sama da 15 ana yi.

Mayakan sa kai a lokacin faruwar lamarin,na rakiyar ayarin fararen hula ne da suka taso daga garin Gamboru na jihar Borno, zuwa Maiduguri babban birnin yankin, a lokacin da motarsu ta taka nakiya da ake zargin mayakan boko Haram ne suka sanya a kauyen Damno, kamar yadda majiyoyin suka bayyana. .

“Tayoyin bayan motar da ke dauke da ‘yan sa kai 13 yan lokuta da wuce wani katon rami da aka binne wata nakiya a cikinsa wadda ta fashe,” in ji Shehu Mada, shugaban mayakan sa kai a Gamboru. “Mutane 11 da ke cikin motar sun mutu, biyu kuma sun jikkata.”

An fitar da wadanda abin ya rutsa da su ne daga ragowar motar kuma aka mayar da su Gamboru domin yi musu jana’iza kamar yadda wani dan banga Usman Hamza ya bayyana.

Hare-haren yan bindiga sannu a hankali ya ragu matuka a Najeriya a tsawon lokacin da sojoji ke kai wa mayakan jihadi farmaki.

Hanyar da ta hada Gamboru zuwa Maiduguri hanya ce mai nisan kilomita 140 don kasuwanci ga yankin da dangantakarsa da makwabciyarta Kamaru.

An sake bude hanyar ne a watan Yulin 2016, bayan da sojoji suka rufe tsawon shekaru biyu saboda hare-haren da mayaka masu ikirarin jihadi ke kaiwa.

RFI

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here