Dalilan da ya sa muka cire tallafin mai – Tinubu

0
224
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Mun cire tallafin mai ne gudun kada Najeriya ta samu karayar tattalin arziki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fada a karshen makon da ya gabata a taron da ke duba tattalin arzikin duniya.

Shugaba Tinubu na halartar taron ne wanda ke gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

“Dangane da batun cire tallafin mai, babu haufi mataki ne da ya zama wajibi a dauka saboda kada kasata ta samu karayar tattalin arziki.” Tinubu ya fada a gaban taron da ke duba tattalin arzikin duniya kamar yadda Channels ya ruwaito.

A shekarar da ta gabata jim kadan bayan da aka rantsar da shi, Tinubu ya cire tallafin mai da gwamnati ke biya wanda ke saukaka farashin mai ga al’umar kasar .

Tinubu ya kara kare matakin da gwamnatinsa ta dauka, yana mai cewa akwai bukatar Najeriya ta kara saita akalar tattalin arzikinta dalili kenan da ya sa aka dauki matakin janye tallafin man.

Tun bayan da aka janye tallafin man a Najeriya, farashin mai a sassan kasar ya tashi lamarin da ya sa farashin kayayyaki musamman na masarufi suka yi tashin goron zabi.

Hakan kuma ya jefa al’umar kasar cikin mummunan yanayi kamar yadda rahotanni ke cewa.

Sai dai Tinubu ya fadawa taron cewa tuni gwamnatinsa ta fara daukan matakan rage radadin da jama’a suke fuskanta sanadiyyar cire tallafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here