Tinubu ya nada shugaban asusun bai wa dalibai bashin karatu

0
108
Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin Jim Ovia, CFR a matsayin shugaban asusun bai wa ɗalibai bashin karatu.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce yana da yaƙinin mista Ovia zai yi amfani da ƙwarewarsa ta aiki wajen ganin ɗaliban ƙasar sun samu damar faɗaɗa karatu ta hanyar samun bashi daga shirin da gwamnatinsa ta ɓullo da shi.

Mista Ovia – wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, kuma ɗan kasuwa – na da digiri na biyu a fannin kasuwanci daga kwalejin kasuwanci ta Harvard da ke Amurka.

Bai wa ɗalibai bashin karatu wani shiri ne da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi, don bai wa ɗalibai damar yin karatu a manyan makarantun ƙasar tare da samun cikakkiyar ƙwarewa, musamman tsakanin matasan ƙasar.

Shugaba Tinubu ya yi fatan cewa mista Ovia zai gudanar da ayyukansa don tabbatar da cewa ɗaliban ƙasar sun samu ƙwarewar da suke buƙata, a duka fannonin ilimi.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shirin kafa asusun bai wa ɗaliban ƙasar bashi don ci gaba da karatunsu, a wani mataki na sauƙaƙa wa ɗalibai raɗaɗin ƙarin kuɗin makaranta da jami’o’in ƙasar suka yi.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here