Abubuwa 3 da gwamnonin Arewa suka cimma a taronsu na Kaduna

1
250

Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta kammala taron da ta gudanar a jihar Kaduna, wanda ya samu halartar kusan dukkan gwamnonin yankin 19. 

Wannan ne karon farko da gwamnonin suka yi irin wannan tattaunawar a 2024. 

Ƙungiyar Northern Governors’ Forum (NGF) ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ta cimma ƙudirori 13 a taron.

Ga manya uku daga cikinsu

1. Ƙungiyar ta lura cewa kyautata rayuwar al’umma na da muhimmanci wajen cigaban yankin, kuma ta damu da yadda adadin yaran da ba su zuwa makaranta ke ƙaruwa a yankin. Wannan dalilin ya sa gwamnonin suka yanke shawarar kuɗaɗe masu yawa a ɓangaren ilimi, da koya sana’o’i, da kiwon lafiya don daƙile matsalar

2. Gwamnonin sun karɓi rahoton kwamatin da aka kafa kan farfaɗo da kamfanin New Nigeria Development Company. Ƙungiyar ta amince cewa mambobinta za su yi nazarin rahoton kafin haɗuwarsu ta gaba

3. Zauren taron ya ce sauyin yanayi, da dabarun noma marasa ɗorewa, da yawan al’umma na kawo wa yankin ƙalubale. Saboda gwamnonin suka amince da ɗaukar matakin kyautata muhalli, dabarun noma masu ɗorewa don kare rayuwa da dukiyoyin mutane da kuma kare rayuwar masu zuwa nan gaba

BBC

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here