‘Nan da kwana uku za mu magance wahalar man fetur a Najeriya’ – Gwamnati 

0
143
Man fetur a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce nan da kwana uku ko biyar za ta kawo ƙarshen tsada da kuma wahalar mai da ake fama da ita a faɗin ƙasar.

Hakan ya biyo ziyarar da manyan jami’an bangaren man fetur na ƙasar suka kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.

Yayin ziyarar, jami’an sun tattauna da manajojin gidajen man domin tabbatar da suna da isasshen kayan da za a ci gaba da sayarwa a nan gaba.

Maijidda Abdulƙadir ce babbar jami’ar yankin arewa maso tsakiyar Najeriya ta hukumar kula da sarrafa man fetur da tacewa da sufuri ta Najeriya (NMDPRA), kuma ta yi wa manema labarai ƙarin bayani kan dalilin ziyarar tasu.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here