Hamas ta amince da sharudan yarjejeniyar tsagaita wuta

0
58
Hamas

Jagorancin ƙungiyar Hamas ya ce sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani na ƙasashen Qatar da Egypt dangane da shawarar amincewar.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani dangane da yarjejeniyar da suka haɗa da tsawon lokacin tsagaita wuta da kuma makomar mutanen da Hamas suka yi garkuwa da su a Gaza.

Jami’an ƙungiyar ta Hamas na cewa yanzu zaɓi ya ragewa Isra’ila tunda su sun amince da sharuɗɗan yarjejeniyar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, shugaban Hamas, Isma’il Haniyeh ya kira firaiministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani da kuma ministan bayanan sirri na Egypt, Abbas Kamel inda ya sanar da su dangane da amincewar da Hamas ɗin ta yi gar yarjejeniyar tsagaita wuta.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here