Ministan harkokin cikin gida na Isra’ila mai ra’ayin riƙau ya yi allah wadai da matakin da shugaba Biden ya ɗauka na ƙin samar da makaman Amurka da za a iya amfani da su a gagarumin farmakin da Isra’ila za ta kai kan birnin Rafah.
Itamar Ben Gvir ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa Hamas na ƙaunar Biden amma Shugaban kasar Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana kalaman ministan a matsayin masu nuna rashin dattaku.
Da yake jawabi yayin bikin tunawa da nasarar da aka samu a kan Jamus a yaƙin duniya na biyu, Mista Herzog ya gode wa shugaba Biden da Amurka kan goyon bayan da ƙasarsa ke samu.
Wakiliyar BBC ta ce rahotanni daga kafofin yada labaran Isra’ila na nuni da cewa jami’an tsaron ƙasar sun nuna matuƙar damuwa kan shawarar da babbar ƙasa mai samar masu da makamai ta ɗauka domin hakan na iya kawo cikas a ɓangaren tsaron Isra’ila.
BBC