Mahamat Idriss Deby  ya lashe zaben kasar Chadi

0
160

Hukumar zaben kasar Chadi ta bayyana cewa shugaban kasar na riƙon ƙwarya Mahamat Idriss Deby Itno ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da sama da kashi 61% na ƙ=kuri’un da aka kada, bayan da babban abokin hamayyarsa ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben. 

Gwamnatin mulkin sojan Chadi ta zama ta farko a cikin Ƙasashen Yammacin Afirka da aka yi wa juyin mulki da nufin komawa kan tsarin mulkin kasar ta hanyar akwatin zabe, sai dai wasu jam’iyyun adawa sun yi ta ƙorafi kan maguɗin zaɓe. 

An girke jami’an tsaro da dama a manyan tituna a babban birnin N’Djamena gabanin bayyana sakamakon zaben, saboda yadda hankula ke ta tashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here