Yan bindiga sunyi awon gaba da dalibai a jami’ar Kogi

0
197

A ranar Alhamis da daddare ne ƴan bindiga suka mamaye jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Okene a jihar Kogi inda suka sace wasu ɗalibai.

Wani shaida ya ce ƴan bindiga sun kutsa jami’ar cikin dare yayin da wasu ɗalibai ke karatu domin shiryawa jarrabawar da ke tafe.

Majiyar ta ce ƴan bindigar sun shiga jami’ar ne ta daji inda suka shiga ɗakunan karatu uku tare da buɗe wuta.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya ce majiyar ta bayyana cewa ƴan bindigar sun tsare ɗaliban a ajujuwansu inda suka riƙa ɗibansu, “an jefa makarantar cikin ruɗani yayin da ɗalibai cikin fargaba a wasu ajujuwan suka nemi mafaka, suka kuma watsu zuwa wasu wuraren jami’ar.”

A cewar majiyar, ɗaliban na shiryawa jarabawar zango na farko da za a soma ranar 13 ga watan Mayu, lokacin da ƴan bindigar suka afka masu.

Shugaban jami’ar, Farfesa Abdulrahman Asipita, ya tbbatar da faruwar lamarin sai dai bai ce komai ba game da adadin ɗaliban da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su.

Ƙoƙarin ji daga kwamishinan ƴan sandan Kogi, Mista Bethrand Onuoha, bai yi nasara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here