Gwamnatin Sokoto zata siyar da abinci a farashi mai sauki

0
38

Gwamnatin Sakkwato ta fara shirin sayar da kayayyakin abinci a farashi mai sauki ga al’ummar jihar.

Gwamnatin tayi shirin za ta sayar da kayan abincin ta hanyar rage kashi 55 cikin dari na kudin kayan da ta sayo Naira biliyan 14.

Gwamnan jihar Ahmed Aliyu ne, ya sanar da hakan a lokacin da yake kaddamar da kwamitin bibiya da sa ido a kan sayar da kayan abincin a ranar Litinin.

Gwamnan, ya ce sun dauki matakin siyar da abincin a saukake domin rage wa mutane radadin da suke ciki na matsin rayuwa tun bayan cire tallafin man fetur.

Yace abincin zai kai dukkanin mazabun jihar 244.

Ya roki yan kwamitin siyar da abincin dasu guji sanya bambancin siyasa ko addini wajen sayar da kayayyakin abincin, inda yace abinci ne na dukkanin jama’ar Sakkwato.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da tallafi irin wannan har zuwa lokacin da tattalin arzikin kasa zai bunkasa kowa ya dogara da abinda yake samu.

Kayan abincin da za’a siyar akan farashin mai sauki sun hadar da shinkafa da sauran kayan masarufi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here