INEC ta saka ranar zaben gwamnan jihar Anambra

0
57

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta saka ranar 8 ga watan Nuwamba 2025 a matsayin ranar gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, ne ya sanar da hakan a birnin tarayya Abuja, lokacin gudanar da wani taron tuntuba tsakanin hukumar INEC da jam’iyyun siyasa.

Karanta karin wasu labaran:EU ta tallafa wa INEC da kayan aiki don inganta harkokin zabe a Najeriya

Yakubu, yace INEC zata sanar da lokacin zaben a hukumance ranar 13 ga watan Nuwamba na shekarar 2024, don yin biyayya ga dokar zabe da ta umarci bayar da wa’adin kwanaki 360, gabanin gudanar da zabe.

Idan za’a iya tunawa an gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.

INEC tace jam’iyyu zasu yi zaben cikin gida a tsakanin watan Mayu zuwa Afrilu na 2025, sai yakin neman zabe da za’a fara a watan Yuni sannan a kammala a 6 ga watan Nuwamba 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here