EU ta tallafa wa INEC da kayan aiki don inganta harkokin zabe a Najeriya

0
161

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta samu kyautar wasu kayan aiki daga ƙungiyarTarayyar Turai ta EU, da za su taimaka wajen inganta harkokin zaɓen ƙasar.

Shugabanb hukumar zaɓen ƙasar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, lokacin karɓar kayayyakin a Abuja bban birnin ƙasar.

Farfesa Yakubu ya ce sabbin kayan aikin za su taimaki hukumar zaɓen ƙasar wajen inganta harkokin zaɓenta.

Yav ƙara da cewa akwai wasu ƙarin kayayakin masu yawa da ƙungiyar EU za ta bai wa hukumar tasa.

”Waɗannan kayayyaki za su taimaka wa hukumar zaɓen wajen inganta harkokinta a ɓangarori da dama”, in ji shugaban hukumar.

Kungiyar ta EU dai na daga cikin kungiyoyin da ke sanya idanu a zaɓuklan Najeriya, inda a lokuta da dama, ƙungiyar ke cewa ana tafka kura-kurai a tsarin zaɓukan ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here