Tankar mai ta kuma fashewa a jihar  Ogun

0
79

Wata tankar man fetur da ta yi hatsari safiyar Laraba ta kona gidaje da motoci tare da jikkata mutane biyu a garin Ibafo da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun.

Tankar man ta kama da wuta ne a wani gari da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

Karanta karin wasu labaran:Fashewar tankar mai ta kashe fiye da mutane 100 a Jigawa

Shaidun gani da ido sun ce, tayar tankar ce ta fashe, wanda hakan ya yi sanadin faduwar motar.

Tankar ta fashe bayan faduwa inda ta lalata gidaje da ababen hawa da ke kusa da wajen data yi hatsarin.

Akalla motoci biyar da suka hada da manyan motoci sun lalace yayin da wasu mutane biyu suka samu raunuka.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta, Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi, ya ce, ba a samu asarar rai ba a lamarin.

Idan za’a iya tunawa an samu makamancin Wannan hatsari a jihar Jigawa cikin daren Talata, inda faduwar tankar mai tayi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da dari a karamar hukumar Majiya.

Gobarar motar man ta kashe mutane da har yanzu ba’a tantance yawan su ba, bayan asarar dukiyar da aka tafka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here