APC ta lashe daukacin zaben kananun hukumomi a Kogi

0
31

Hukumar zaben jihar Kogi ta sanar da jam’iyyar APC mai mulkin jihar a matsayin wadda ta lashe daukacin zaben shugabannin kananan hukumomin jihar 21 da aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban hukumar  Mamman Nda-Eric wanda ya ayyana haka, ya ce zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci.

Gwamnan jihar ta Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben da kuma yadda yan jihar suka kasance cikin nutsuwa tare da zabar abin da suke so ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, cewar sa.

Karanta karin wasu labaran:Yan bindiga sunyi awon gaba da dalibai a jami’ar Kogi

Sai dai jam’iyyun adawa a Kogi kamar PDP da CNPP sun yi zargin cewa ba’a bi ka’idar dimokuradiyya a zaben ba.

Sun ce ba a gudanar da wani sahihin zabe a jihar ba, inda suka ce hukumar zaben ta sake nuna gazawarta wajen shirya sahihin zabe.

Daman sanin kowa ne a Nigeria duk jam’iyyar da take mulki a jiha itace ke lashe daukacin zaben kananun hukumomi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here