Hukumar zabe ta jihar Kano ta fara rabon kayan aikin zaben kananun hukumomi

0
92
Kano

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC ta fara rabon kayan aikin zaben kananun hukumomi da za’a gudanar ranar asabar mai zuwa.

Kwamishinan hukumar mai kula da harkokin majalisa da kafafen yada labarai, Lawan Badamasi, ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Kwamishinan yace tuni suka rarraba kayan zabe zuwa mazabu, za kuma a fara rabon kayan zabe masu muhimmanci daga yau alhamis zuwa juma’a.

Yace za’a fara gudanar da zaben daga karfe 8:00, na safiyar ranar asabar zuwa 2 na rana.

Lawan Badamasi, yace ko yan sanda basu halarci zaben ba, za’a yi amfani yan KAROTA da Hisbah, ko yan Bijilanti.

Kwamishinan yace an samar da shugabannin hukumar KANSIEC a karkashin tsarin doka, sabanin yanda wata kotun tarayya tace ba’a dora shugabannin KANSIEC mukamin su akan ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here