Kamfanin rarraba lantarki TCN yace ya gano daga inda matsalar wutar lantarkin arewacin Nigeria take, tare da daukar matakin gaggawa don gyara wutar.
A ranar talata ne kamfanin TCN ya tabbatar da lalacewar turken lantarkin daya kawo wutar arewa wanda hakan ya haifar da babbar matsalar rashin wutar, wadda aka dauke a jihohin arewa tun ranar litinin data gabata.
Karanta karin wasu labaran:Majalisar wakilai ta bayar da umarnin bincikar yawan lalacewar lantarki
A ranar Laraba manajar hulda da jama’a ta TCN Ndidi Mbah, tace an gano matsalar lantarkin daga dajin Igumale dake jihar Benue.
Tace bayan gano matsalar kamfanin TCN ya shirya fara gyara a yau alhamis