Lalacewar jirgi ta hana Kashim Shettima wakiltar Nigeria a taron Commonwealth

0
58

Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya fasa zuwa taron kungiyar kasashe renon Ingila ta Commonwealth na 2024 dake gudana a tsibirin Samoa, bayan da jirgin sa ya samu matsala a lokacin da ya sauka a Amurka.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar ya ce a lokacin da jirgin ya yada zango a birnin New York na Amurka, wani abu ya daki jirgin wanda kuma ya lalata gilashin direban jirgin.

Karanta karin wasu labaran:Kashim Shettima zai wakilci Tinubu a taron Commonwealth

Sanarwar ta ce tuni shugaba kasa Bola Tinubu ya amince da shirya wata tawagar ministoci, karkashin jagorancin ministan muhalli, Balarabe Abbas Lawal domin wakiltar Najeriya a taron, yayin da ake ci gaba da gyaran jirgin mataimakin kasar.

An fara taron a ranar 21 ga watan Oktoba, wanda ake sa ran kammala shi ranar 26 ga watan Oktoba a tsibirin tekun Pacific.

Sanarwar ta ce Kashim Shettima tare da tawagarsa da ta kunshi ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar sun kama hanyar dawowa Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here