Jega ya nemi gwamnatin Nigeria ta dena amincewa bankin duniya

0
64

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeria Farfesa Attahiru Jega, ya nemi gwamnatin tarayyar Nigeria ta dena amincewa duk wata shawarar da hukumomin bayar da lamunin kudi na duniya suke bata musamman bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya IMF.

Yace duk da cewa akwai wani amfanin da za’a iya samu ta hanyar yin ma’amala da hukumomin amman in akayi wasa zasu jefa Nigeria matsalar da za’a jima ba’a fita ba.

Farfesa Jega, ya bayyana hakan a yau lokacin da yake jawabi a wajen taron shekara shekara akan kyakyawan shugabanci, wanda Cibiyar daraktocin harkokin kudi ta Nigeria ke shiryawa.

Ya Kuma nemi ayi gyaran fuska ga yanayin shugabanci a Nigeria, inda yace a yanzu matsalar da Nigeria ke ciki ita ce shugabannin ta basu shirya yin shugabanci na gari ba.

Mafi yawancin al’ummar Nigeria sun zargi hukumomin bayar da lamuni da duniya da cewa su suka angiza shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya kara farashin man fetur.

Amman a kwanakin baya shugabancin asusun bayar da lamuni na duniya, reshen Afrika yace babu hannun su a cire tallafin man fetur din da Tinubu yayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here