Gwamnan Kano yasha alwashin kubutar ‘ya’yan Jihar da gwamnatin tarayya ta gurfanar

0
46

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya dauki aniyar yin duk mai yiwuwa don kubutar da kananun yaran da gwamnatin tarayya ta gurfanar akan zargin yunkurin kifar da Gwamnatin.

An kama kananun yaran lokacin gudanar da zanga zangar neman shugabanci na gari da ta wakana a watan Ogusta na wannan shekara.

Daga cikin kananun yaran da aka kama akwai yan asalin jihohin Kano, Kaduna, Plateau, Gombe, Katsina, da birnin tarayya Abuja, sannan ana zargin su da aikata lefukan ta’addanci, cin amanar kasa da sauran su.

An gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja, ranar juma’a.

An samu hudu daga cikin kananun yaran da suka sume a kotun saboda azabtarwar da aka yi musu da kuma barin su a cikin yunwa.

Wani abu da kotun tayi na bayar da belin kowanne yaro daya akan naira miliyan 10, da karin wasu sharudan ya nuna cewa ba da gaske ake son bayar da yaran beli ba.

Gurfanarwar ta haifar da yin ala wadai daga fadin Nigeria har da sauran kasashen duniya, sakamakon cewa za’a iya yi musu afuwa saboda karancin Shekarun su.

Amman a wani batu da lauyan gwamnatin tarayya a shari’ar Rimazonte Ezekiel, yayi na cewa wadanda aka gurfanar ba yara bane, wai a cewar sa wasu daga cikin su suna da aure, amma duk mai hankali yasan ba haka zancen yake ba, musamman in ka kalii hotunan kananan yaran.

Sannan kalaman lauyan ya saba da batun kakakin rundunar yan sandan kasa Muyiwa Adejobi, wanda yace yaran yan shekaru 13 zuwa kasa ne.

Abba Kabir Yusuf, yace zuwa yanzu an bawa kwamishinan shari’a na Kano umarnin lalubo hanyar da za’a taimakawa yaran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here