Gwamnan Kano ya bijirewa kiran wayar Kwankwaso

0
95

Rikicin cikin gida na neman mamaye jam’iyyar NNPP a matakin jihar Kano, tun bayan bayyanar wata kungiya mai suna Abba tsaya da kafar ka.

Ita dai Wannan kungiyar na neman gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya dena yiwa Kwankwaso biyayya akan wasu abubuwan sha’anin mulkin sa.

A cewar jaridar Daily Nigerian, Gwamna Abba Yusuf ya yi fatali da wasu tarurruka da kuma kin amsa kiran wayar mai gidan sa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A wannan lokacin tuni wasu yayan jam’iyyar NNPP da suka hadar da masu rike da mukamai suka fara nunawa Kwankwaso yasha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here