Gwamnatin Kano ta fara yiwa yan kasar waje mazauna jihar rijista

0
71
Kano

Gwamnatin Kano ta dauki hanyar yiwa daukacin yan kasar waje mazauna jihar rijista da Kuma daukar bayanan kasuwancin da suke yi, tare da tantance su.

Shirin wanda yake karkashin ofishin sakataren gwamnatin Kano an Samar da shi da manufar inganta tsaro da bin dokokin kasa.

Mai magana da yawun kwamitin dake aikin tantance yan kasar wajen, yace suna yin hakan don tsaftace harkokin kasuwanci da tsaro, daga bangaren yan kasa har zuwa mutanen ketare.

Kwamitin ya yabawa yan kasar waje masu sana’o’i a kasuwar kantin kwari, bisa bayar da hadin kai ga kwamitin ba tare da tangarda ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here