An sace mutane 50, a Zamfara, tare da neman fansar miliyan 150

0
82

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane fiye da 50 a wasu kauyukan Jihar Zamfara, yayin da suke tsaka aikin gona.

Yan ta’addan sun kuma sanya wa mazauna kauyukan harajin Naira miliyan 50 ga kauye guda daya, wanda suka bayar da wa’adin mako biyu kacal akan su tattara kudaden.

Bayan haka sun sanya tatar sama da Naira miliyan 100 a kan wasu kauyuka da ke Karamar Hukumar Tsafe.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ’yan fashin daji a kan babura ne suka yi awon gaba da manoma sama da 50 a kauyukan Gusau da Gummi.

Mutanen da aka sace su 50, ciki har da wani limami, wanda karo na biyu ke nan da ake sace shi.

An yi garkuwa da mutanen ne a yayin da suke tsaka da aiki a gonakin su a yankin Wanke da kewaye, da ke kan hanyar Anka zuwa Gurusu a Ƙaramar Hukumar Anka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here