Sojojin Nigeria sun sha alwashin kawo karshen sabuwar Kungiyar yan ta’adda data shigo Sokoto 

0
79

Shalkwatar tsaro ta  Najeriya ta tabbatar da kafuwar wata kungiyar lakurawa wadanda suke tayar da hankalin al’umma a tsakanin jihohin Sokoto da Kebbi.

Daraktan yada labarai na shalkwatar ne ya tabbatar da hakan, inda ya kara da cewa suna da masaniya akan bullar kungiyar a Sokoto da Kebbi.

Yara cewa kungiyar ba za ta yi wani tasiri ba, domin a cewarsa sojojin Najeriya a shirye suke, kuma za su ga bayansu cikin karamin lokaci.

Lakurawa wata kungiya ce ta yan bindiga da suka fara addabar mutanen Sokoto da Kebbi, kuma sun fito ne daga bangaren yankin Sahel da ya kunshi kasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka kunshi ƙabilu daban-daban na kasashen yankni Sahel.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here