Shugaban Nigeria Tinubu zai halarci taron G20

0
45

Nan bada jimawa ba shugaban Nigeria Bola Tinubu, zai bar kasar domin halartar taron shugabannin kasashe 20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya wanda zai gudana a kudancin Amurka.

Mai taimakawa shugaban a fannin yada labarai da tsare tsare Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a yau cikin wata sanarwa daya fitar.

Tafiyar tazo kwanaki biyar bayan dawowar sa daga kasar Saudiyya, daya halarci taron shugabannin Kasashen Musulman duniya, daya gudana a birnin Riyadh.

Onanuga, yace Tinubu zai bar Nigeria a yau lahadi, don halartar taron G20, karo na 19.

Za’a fara gudanar da taron a gobe litinin zuwa Talata, wanda za’a tattauna akan batutuwan da suka shafi kasuwanci da tattalin arzikin kasashe.

Shugaba Tinubu zai yi tafiyar tare da rakiyar wasu jami’an gwamnatin sa ciki har da ministan harkokin waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here