Karancin bayar da takardun kudi ya fara ta’azara a bankuna

0
51

Wani bincike ya bayyana cewa ana fuskantar matsalar rashin isassun takardun kudi a bankunan Nigeria, wanda hakan yake kawo koma bayan hada hadar kudi musamman a wajen masu kananun sana’o’i da basu fiya amfani da bankuna ba.

Wani mai ma’amala da bankuna wanda jaridar Daily News 24, ta zanta da shi a yau litinin, a jihar Kano, yace lamarin cirar takardun kudi a bankuna ya zama babbar wahala.

Yace ko da yaje cirar kudi a daya daga cikin bankunan Nigeria bai samu ba, inda akace sai dai a tura masa kudin zuwa wani asusun amma ba zai samu kudin a hannu ba.

Umar Muhammad, yace duk da yana bukatar kudin a hannu haka ya hakura tare da zuwa a tura masa kudin zuwa wani asusun.

Wasu mutanen kuma sun ce in aka ciri wani adadin kudin a mako shikenan sai wani makon mutum zai samun damar cirar wasu kudin.

Masu fashin baki na daukar hakan a matsayin wani mataki da mahukuntan Nigeria suka dauka na hana bazuwar kudi a hannun jama’a.

Idan za’a iya tunawa an fuskanci matsalar rashin kudi a hannu tun lokacin zaben Nigeria na shekarar 2023, wanda kotu ta yanke hukuncin dena yin amfani da tsaffin kudi, kafin wata kotun da tazo daya baya ta rushe wannan hukunci, kuma hakan ya haifar wa al’umma shan wahalar gaske.

Ko a yanzu ana shan bakar wahala in aka zo fannin neman canji, musamman canjin naira 500.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here