Ma’aikatan Zamfara zasu shiga yajin aiki saboda kin fara biyan mafi karancin albashi

0
71

Mambobin kungiyar kwadago ta Nigeria NLC, reshen jihar Zamfara sun sanar da shirin su na tsunduma yajin aiki, a karshen watan Nuwamba, in har gwamnatin jihar ta gaza fara aiwatar da dokar biyan mafi karancin albashin ma’aikata da gwamnatin tarayya ta amince da shi na naira 70,000.

Karanta karin wasu labaran:Sojoji sun halaka ‘yan bindiga a Zamfara

NLC, tace abun da wasu gwamnonin keyi na kin fara aiwatar da biyan mafi karancin albashin ma’aikata ya bayyana cewa ko kadan basa tausayawa ma’aikatan a daidai wannan lokacin da ake shan wahalar tsadar rayuwa, biyo bayan cire tallafin fetur da tabarbarewar tattalin arziki, wanda hakan ya jefa yan Nigeria da dama a cikin yunwa da fatara.

Tun tuni gwamnatin jihar ta Zamfara ta amince cewa zata biya ma’aikata sabon mafi karancin albashin, wanda har yanzu ta gaza fara aiwatarwa.

Dama uwar kungiyar kwadago ta Nigeria tace zata umarci mambobinta dasu shiga yajin aikin sai baba ta gani a duk jihohin da gwamnonin su suka kasa aiwatar da sabuwar dokar albashin ta naira dubu 70,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here