Darajar Bitcoin daya ta zarce Dala dubu 97

0
54

A karon farko cikin tarihin kasuwar crypto, a yau alhamis an samu gagarumar nasara inda kowanne Bitcoin daya darajar sa ta zarce Dala dubu 97, sannan ta zarce naira miliyan 169,750,000, a kudin Nigeria.

Hakan baya rasa nasaba da nasarar Donald Trump, ta lashe zaben shugaban kasar Amurka, zaben 5 ga Nuwamba, wanda tun lokacin farashin Bitcoin yake tashi babu tsayawa.

Trump, ya kasance mai goyon bayan harkokin kasuwancin Crypto, yayin da Kamala Harris, da suka yi takara da tare bata goyon bayan harkokin crypto.

Dama anyi hasashen cewa in har Trump, ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, kasuwar crypto zata samu alkairi masu yawa, saboda yayi alkawarin taimakawa crypto, kuma shima daya ne daga cikin manyan yan crypto na duniya.

Daga yanzu zuwa ko yaushe za’a iya ganin darajar kowanne Bitcoin daya ta zarce Dala dubu 100.

Ana hasashen cewa harkokin crypto zasu cigaba da samun nasara har bayan rantsar da Donald Trump, a matsayin shugaban Amurka a watan Junairu na 2025.

A daidai lokacin rubuta Wannan labari darajar kowanne Bitcoin daya tana kan dala 97,4895.4.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here