Mataimakin shugaban kasar Nigeria Kashim Shettima, yace zuwa yanzu kasar ta fara farfadowa daga matsalolin matsin tattalin arzikin da suka dabaibaye ta.
Shettima ya ce yanayin habbakar tattalin arzikin cikin gida na kasar wato GDP ya karu da kaso 2.98 a watanni 3 na farkon shekarar 2024.
Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa, Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin bude kasuwar duniya ta Legas.
A cewar sa tsare tsare da shugaban Kasa Tinubu ke bijirowa dasu ne ke habbaka tattalin arzikin.
Shettima, wanda mai taimaka masa na musamman kan ci gaban yankuna, Dr Marian Tomitope Marshall ta wakilta, ya buƙaci waɗanda za su halarci kasuwar duniyar su yi amfani da damar da suka samu domin kawo hanyoyin inganta tattalin arziki.
Ya ce gwamnatin Tinubu tana kokarin samar da hanyoyin saukaka harkokin kasuwanci, don inganta walwalar kasuwanci a Nigeria da ketare.