Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai Aliyu Sani Madakin Gini, ya zargi jagoran jam’iyyar su ta NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da kitsa makarkashiyar cire shi daga mukamin, na mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Ali Madaki, ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da Kafar yada labarai ta Daily Nigerian.
Yace abin dariya ne, ace Kwankwaso ya hada kai da wasu yan majalisar da ba yan jam’iyyar NNPP bane da cewa su cire shi daga mukamin.
Yace tun tuni shugabancin jam’iyyar NNPP na kasa ya kori masu shirya cire shi, sannan yace mutanen da suke yin hakan suna daukar maganar Kwankwaso a matsayin wadda tafi ta kowa muhimmanci.
A cewar Ali, mutanen da suka sanya hannu akan takardar dake neman a raba shi da mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai ba yan jam’iyyar NNPP bane, yana mai cewa shi kansa Sanata Kwankwaso, ba’a jima ba kotu ta kore shi daga NNPP.
Rikicin cikin gida da jam’iyyar NNPP ke fama da shi ne ya kawo baraka tsakanin Aliyu Sani Madakin Gini, da uban gidan sa Sanata Kwankwaso.