Gwamnatin Yobe ta bawa masu ambaliya da yan kasuwa tallafin kusan biliyan 3

0
25

Gwamnatin jihar Yobe, ta samar da shirin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa da yan kasuwa don inganta harkokin su na yau da kullum da kuma rage musu asarar da suka tafka.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, shine ya kaddamar da rabon tallafin na Naira biliyan 2.93 ga mutane 40,000.

Buni ya ce, mutane 25,000 daga cikin waɗanda suka amfana su ne wadanda ambaliyar ruwa a shekara ta 2024 ta shafa da kuma marasa galihu, ragowar mutun 15,000 kuma ƙananan ’yan kasuwa ne.

Ya kara bayyana cewa manufar taron itace kaddamar da shirye-shiryen tallafin gwamnatin jihar don karfafawa ‘yan Jihar da suka gamu da Iftila’in ambaliyar ruwan da kuma taimakawa kananan ‘yan kasuwa su kara habaka harkokin su na kasuwa.

Ya ce, kimanin mutane 441 a faɗin kananan hukumomi 17 abin ya shafa, inda sama da magidanta 20,000 suka rasa matsugunansu.

Bayan wannan yace jihar ta Yobe, ta rasa rayukan mutane 34 sakamakon ambaliyar, wasu 386 kuma suka jikkata, sannan sama da mutane 50,000 sun rasa hanyoyin gudanar da rayuwa.

Gwamnan ya ce, kowane ɗaya daga cikin mutane 25,000 da ambaliyar ruwan ta shafa da marasa galihu za su samu tallafin Naira 50,000, yayin da aka ware Naira 100,000 ga kowanne daga cikin ƙananan ’yan kasuwar su kusan 15,000.”

Buni ya ce gwamnatinsa ta gyara muhimman hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata, a yayin da Gwamnatin Tarayya da sauran su suka raba tsabar kuɗi Naira miliyan 100 ga waɗanda ambaliyar ta shafa baya ga kayan abinci da aka raba tun da farko a yankunan da lamarin ya fi ƙamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here