Sai albashi ya gagari arewa in dokar harajin Tinubu ta fara aiki—-Zulum

0
74

Gwamnan jihar Borno ya ce za su hada kan ‘yan majalisar dokoki daga Arewacin Najeriya domin yakar dokar karin haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu yake son a gaggauta amincewa da ita.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce dokar za ta kassara Arewacin kasar sannan kuma ta daukaka tattalin arzikin jihar Legas.

A hirarsa da BBC, gwamnan jihar Borno, ya ce bai kamata gwamnati ta nuna bukatar ‘yan majalisar dokoki kasar su hanzarta amincewa da dokar ba.

Sannan ya ce abin da ke daure musu kai shi ne yadda ake azarɓaɓin ganin kudirin dokar ya soma aiki nan ba da jimawa ba.

Gwamna Zulum da ke tir da wannan kudiri, ya tunasar da cewa akwai kudirori a baya da suka shafe shekaru ana jayayya a kai, me ya sa a wannan lokaci ba za a natsu a fahimci kudirin ba kafin ta zama doka.

Zulum ya bi sahun takwarorinsu gwamnonin arewa da masu adawa daga yankin da ke jadadda cewa an kirkiro wannan kudiri ne domin a raya Legas mahaifar Tinubu.

Sannan ya ce ko a yankunan kudancin Najeriya akwai shiyoyyi irinsu Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da ba murna suke da wannan doka ba.

Gwamnan ya nuna akwai fargaba da yiwuwar a samu wasu ‘yan majalisa da za su goyawa kudirin baya, shiyasa suka fito suna ankararwa da jan hankalin mambobinsu da ma sauransu su yi hattara.

Gwamnan ya ce ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu tuna cewa Arewa ce ta ba shi kashi 60 cikin 100 na kuri’un da ya samu.

Zulum ya ce lokaci ya yi da ya kamata mutane su farka musamman wakilan arewa domin kare muradanta da al’umma, saboda muddin aka bari wannan doka ta wuce to albashi sai ya gaggaresu.

Sannan gwamnan ya nuna fargabar cewa idan aka yi sakaci kudirin ya zama doka to yunwa da fatara da talauci za su samu wajen sama a cikin al’umma.

Wadannan kalamai na Zulum na zuwa ne bayan wasu jiga-jigai da ‘yan adawa na Arewa ke gargadin wakilansu kada su yi sakaci wannan doka ta samu karbuwa.

Tun dai lokacin da shugaba Tinubu ya aike da wannan kudiri majalisa ake ta cece-kuce tsakanin rukunnin al’umma da manyan ‘yan siyasa musamman gwamnoni akan wannan kudiri da yadda za ta mayar da arewacin kasar baya.

Bayanai na cewa shugabannin majalisun na ci gaba da wani zaman tattaunawa domin shawo kan sauran Æ´an majalisar su amince da kudurin dokar, wanda shugaban kasa ke neman a gaggauta domin ta soma aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Ƙudurin dokar dokar ya ce ba za a buƙaci mutanen da ke samun kudaden da suka yi kasa da naira 800,000 a shekara su biya haraji kan wadannan kudaden ba, har sai kuɗin da ake samu a shekara ya kai milaiyan 2.2 kafin ya fara biyan harajin kashi 15 cikin 100 a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here