Shugaban hukumar zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC za ta yi dukkan abin da za ta iya domin tabbatar da a lokacin zaɓen gwamnoni an kauce wa maimaita duk wasu cikas ɗin da aka fuskata lokacin zaɓen shugaban shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.
Yakubu ya yi wannan jaddadawa ce a lokacin da ya ke taro da Kwamishinonin Zaɓe na Ƙasa, domin bibiya da nazarin yadda hukumar ta gudanar da zaɓen 25 ga Fabrairu, 2023.
Ya ce maƙasudin taron na su shi ne a tattauna cikas ɗin da aka samu da kuma tabbatar da cewa ba a sake maimaita faruwar haka a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi ba, wanda za a gudanar a ranar 11 ga Maris, 2023.
“Babu shakka zaɓen da aka gudanar a satin da ya gabata ya samu cikas da ƙalubalen da ke buƙatar magancewa da kuma hana sake afkuwar su da gaggawa. An ɗauki lokaci tare da shan matuƙar walaha wajen tsare-tsaren yadda za a gudanar da zaɓe. Amma dai an fuskanci cikas wajen aiwatarwa.
“Waɗansu ƙalubalen da aka ci karo da su, bagatatan su ka faru, ba a yi zato ko tunanin hakan zai iya faruwa ba. Musamman matsalolin aikawa da kayan zaɓe, na’urorin sadarwa da tsarin fasahar zamani, halayyar wasu jami’an zaɓe, ɗabi’un wasu ejan-ejan na jam’iyyu da masu goyon bayan jam’iyyun sun ƙara kawo wa tsarin tafiyar da shirin naƙasu ko cikas.”
Yayin da ya ke yaba wa irin jajircewar da ‘yan Nijeriya su ka yi da halin dattakon da wasu shugabannin siyasa su ka nuna, Yakubu ya ce abin da ya faru a lokacin zaɓe ya zama wani babban darasi ga INEC, ta yadda ta gaggauta gano matsalolin da su ka faru, domin kauce wa sake faruwar irin haka a zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki ta jihohi, wanda za a yi zaɓen gwamnoni a jihohi 28, kuma za a zaɓi ‘yan majalisar dokoki har 996.
Yakubu ya ce a zaɓen ranar tilas ma’aikatan INEC su zage damtse sosai a lokacin zaɓen ranar 11 ga Maris.
“Duk ma’aikacin da aka kama ya na wasa ko rashin ɗaukar aikin sa da muhimmanci, ko na dindindin ne ko na wucin-gadi a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, to kada a kuskura a bar shi ya yi aikin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokoki.
“Tilas kuma ya kasance an kai kayan zaɓe kwanaki kafin ranar zaɓe a dukkan ƙananan hukumomi.
“Kwamishinonin Zaɓe da aka tura jihohi za a ɗora wa laifin rashin kai kayan zaɓe zuwa ƙananan hukimomi da wuri. Haka babu wani dalilin da za a ƙi kai janareto a cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.”
Yakubu ya ce za a tabbatar an yi amfani da na’urar tantance masu rajistar zaɓe, wato BVAS a ranar zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi.