Gwamnatin tarayya ta gayyaci jakadan Burkina Faso kan kisan ‘yan Najeriya 16

0
61

Gwamnatin Najeriya ta fara daukan kwakkwaran matakai domin bankado batutuwan da suke mamaye da kisan ‘yan Najeriya 16 da suka yi niyyar zuwa ziyarar musulunci a Kaolack da ke kasar Senegal da ake zargin jami’an tsaron Burkina Faso ne suka kashe su.

Karamin ministan kula da harkokin cikin gida, Ambasada Zubairu Dada shi ne ya gayyaci jakadan na Burkina Faso Charge D’Affaires Passida Pascal Gouba a Nijeriya kan kisan gilla da aka yi tare da neman bayanin hakikanin abubuwan da suka faru wajen kisan ‘yan Nijeriya 16 da ake zargin sojojin Burkinabe da aikatawa.

A cewarsa, Nijeriya ta damu sosai da wannan lamarin don haka tana bukatar cikin gaggawa a hanzarta samar da amsar tambayoyin da suke yi wa gwamnatin Burkina Faso, a cewar wata sanarwar da hadimin ministan a bangaren yada labarai, Ibrahim Aliyu ya fitar.

Ministan ya nuna matukar kaduwarsa kan lamarin tare da misalta hakan da cewa abu ne da ba za a lamunta ba, kuma babu bukatar bata lokaci wajen samu gaskiyar abubuwan da suka faru cikin lamarin. Ya ce, ahlin mamatan su na ta yin tambayoyi daban-daban kuma su na bukatar a gaggauta yin bincike.

Ministan ya ce, Nijeriya ba za ta nade hannayenta haka nan tana kallo ana cin zarafi da kashe ‘yan kasarta a sassa daban-daban na duniya ba.

A nasa bangaren, ministan harkokin Burkina Faso a Nijeriya, Gouba, ya fara ne a jajanta wa iyalan mamatan tare da gwamnatin Nijeriya hadi da al’ummar kasar bisa abun da ya kira lamari na ban takaici da bakin ciki da ya faru. Ya ce, ya fahimci irin zafi da radadin da iyalan mamatan ke ji.

Ya ce, tunin gwamnatin Burkina Faso ta kaddamar da bincike domin ganowa da fito da asalin wadanda suka aiwatar da wannan kisan, ya kara da cewa a shirye suke su yi aiki tare da kwararrun tawaga daga Nijeriya domin gano hakikan abun da ya faru.

Daga bisani, Ambasada Dada ya kuma gana da wakilan kungiyar Darikar Tijaniyyah a karkashin jagorancin sakatare-janar na kungiyar Malam Muhammad Alkasim, inda ya masa bayani kan lamarin da ya faru tare da bayani kan ganawarsu da jakadan Burkina Fason.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here