Mun gano ’yan siyasar Kano da ke shirin dauko ’yan daba — ’Yan sanda

0
94

’Yan sanda sun gano shirin wasu ’yan siyasa na hayar ’yan daba zuwa Jihar Kano don tayar da rikici a zaben gwamna da ’yan majalisar jiha da ke tafe ranar Asabar.

Da yake sanar da haka, kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya gargadi ’yan siyasar da ake zargi su gaggauta sanin inda dare ya yi musu domin ba su da mafaka a jihar.

A cewarsa, “Ba za mu zuba ido mu kyale wasu su zo su tayar mana da hankali a jihar ba, don haka duk wanda ya tayar da tarzoma a jihar nan, za mu kama shi tare da ubangidansa mu gurfanar da sa a gaban kotu.”

Kiyawa ya jaddada cewa rundunar za ta hada gwiwa da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar da kewayenta.

Ya kuma shawarci al’umma cewa “su sa ido a yankunansu kuma su hanzarta sanar da jami’an tsaro mafi kusa a duk lokacin da suka ga wata bakuwar fuska musamman wadda ba su amince da ita ba, ta hanyar kiran wadannan lambobin waya 08032419754 ko 08123821575 ko09029292926.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here