Dan wasan tsakiya na Juventus, Paul Pogba zai koma wata jinyar, bayan da ya raunata kafarsa a yayin da yake daukar bugun tazara.
Pogba mai shekaru 29 zai yi jinyar kusan makowanni 3, saboda haka ba zai samu fafatawa a wasan neman tikitin zuwa gasar Euro 2024 da kasarsa Faransa za ta fara ba.
Bayan da aka yi wasa babu shi saboda dalilai na rashin da’a a karawar Juventus da Frighburg a wasan gasar Europa League a makon da ya gabata, Pogba bai buga wasan da Juventus ta lallasa Sampdoria da ci da 2 da 0 ba.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce an yi wa Pogba gwaje-gwaje a ranar Litinin, inda aka tabbatar da ya samu matsalar cirar tsoka a cinyarsa.
Juventus za ta koma filin fafatawa a gasar Europa ranar Alhamis na wannan makon ba tare da Pogba ba a wannan karon sakamakon rauni.
Sau biyu kawai ne Pogba ya buga wa Juventus wasa a matsayin canji tun da ya yi mata kome daga Manchester United a kakar da ta wuce.