Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi hukumar zabe ta Kasa (INEC) da yunkuri murde wa jam’iyyarsa nasarar da ta samu a zaben gwamnan jihar Kano.
Kwankwaso wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya yi zargin ne a yayin da ake jiran INEC ta sanar da sakamakon zaben a hukumance, bayan dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusu ya samu kuri’u mafi rinjanye.
A wata hira da aka yi da shi kai-tsaye ta shafin Freedom Radio na Facebook, Kwankwaso ya yi zargin cewa, baturen zaben na neman kago wani abu da zai fake da shi domin sanar da cewa zaben bai kammala ba.
Wannan furuci na da nasasa da lokacin da baturen zaben gwamnan, Farfesa ,,, ya nema domin hada lissafi ya fitar da sakamakon karshe.
Amma Kwankwaso ya ce ‘Wannan awa biyu da [baturen zaben] da ya nema, abin da muke da labari zai je ya yi shi ne, shi ne ya dawo da sabon labari.
“Duk kuri’un nan da daka yi, ya je aka kawo sabon rahoto, … yadda za su yi kokari su sake cewa zabe is ‘inconclusive’, saboda haka sai an sake zabe.
“Saboda haka ranar zabe da suka sa (nan gaba, za) su gayyato mutane daga jihohi, kamar yadda aka yi a wancan (na 2019), a kori kowa su rubuta [sakamakon da suke so],” in ji shi.
A halin yanzu dai INEC ake jira, da zarar ta dawo daga hutu, ta sanar da sakamakon zaben.
Sakamakon farko dai ya nuna Abba Kabir Yusuf na NNPP ke kan gaba, inda ya ba wa abokin takararsa na jam’iyyar APC mai mulkin jihar tazara kuri’u sama da 128,000.
Sai dai INEC ta ce sai an lissafa yawan kuri’un da aka soke da kuma tazarar da aka samu tsakanin manyan ‘yan takarar kafin a sanar da sakamakon.
Idan tazarar ta haura kuri’un da aka soke, to shi ke nan, amma idan kuri’un rumfunan da aka soke sun zarce tazarar, akwai yiwuwar a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Irin haka ta faru a zaben 2019, inda a wancan lokacin Abba ke gaban Gwamna Abdullahi Ganduje na APC, amma da aka sake zaben rumufunan da aka soke, Ganduje ya sha gabansa, ya samu tazarce.