Kamata ya yi zaben Kano ya zama ‘Inconclusive’ – APC

0
101

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yi fatali da sakamakon zaben da ya ba jam’iyyar NNPP nasara, inda ta ce kamata ya yi a bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba, wato ‘inconclusive’.

Jam’iyyar ta sanar da haka ne a yayin wani taron manema labarai da dan takararta a zaben, kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranta a Kano ranar Talata.

Yayin taron dai, Gawuna na tare da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da kuma wakilin jam’iyyar a wajen tattara sakamakon zaben, Rabi’u Sulaiman Bichi.

A cewar mai ba jam’iyyar shawara a bangaren shari’a, Barista Abdul Fagge, APC ta yi Allah wadai da yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar.

Ya ce, “Dogaro da Dokar Zabe ta 2022, kamata ya yi a bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, wato inconclusive, saboda yawan layin zaben da aka karba a yankunan da sossoke zabensu ya haura 270,000, wanda hakan ya haura tazarar da ke tsakanin manyan ’yan takara biyu.

A cewar Ado Doguwa, kin bayyana zaben a matsayin inconclusive ya nuna INEC ba ta da cikakken tsarin gudanar da abubuwa.

Ya ce irin yanayin da hukumar ta yi la’akari da shi, wajen bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba, don haka bai ga dalilin da za ta bambanta wannan ba.

Daga nan sai jam’iyyar ta ba hukumar kwana bakwai ta sake duba sakamakon kamar yadda Dokar Zaben ta tanada.

Shi kuwa Gawuna kira ya yi ga magoya bayansa da su kwantar da hankali yayin da suke ci gaba da nazarin mataki na gaba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here