Barkan mu da sake saduwa a shafinmu na na girke-girke, yau muna tafe da yadda ake yin fada-dukar taliya da kabewa.
Kayan hadi
- Kabewa
- Taliya
- Alayyahu
- Tafarnuwa
- Attarugu
- Tumatir
- Man gyada
- Albasa
- Gishiri
- Kayan dandano
- Ruwa
Yadda ake hadi
A wanke kabewa a yayyanka ta, a ajiye a gefe.
A wake tatasai da albasa da attarugu da tumatir da tafarnuwa sai a markadasu.
A wanke allayyahu da gishiri, a dauraye sosai sai a yanka ta manya, ajiye.
Sai a dora ruwan sanwa, a dafa taliya, a bari sai ta nuna, sai a juye a gwagwa ruwan ya tsane.
A dora tukunya a wuta ba mai yawa ba, a zuba man gyada da markaden da aka yi, a rika juyawa a-kai-a-kai.
Daga nan sai a sanya tumatir a ciki, a ci gaba da juyawa, sannan daga baya a zuba kabewar a ciki.
A zuba kayan dandano a rika juyawa a-kai-a-kai na kimanin minti hudu.
Sai a dauko taliyar a juye a kai, a yi ta motsawa na minti daya ko biyu.
Daga nan sai a saukar daga wuta, sannan a sanya alayyhu a kai.
Shi ke nan sai ci.