Gabanin rantsar da gwamnoni an canja sabbin kwamishinonin ’yan sandan Kano da Kaduna

0
131

Hukumar Aikin Dan Sanda ta nada sabbin kwamishinonin ’yan sanda zuwa jihohin Kano da Kaduna da wasu jihohi 10.

Hukumar ta yi sauyin ne a shirye-shiryenta na tabbatar da tsaro gabanin ranstar da sabuwar gwamnati da ke tafe ranar 29 ga watan Mayu mai kamawa.

Hakan kuwa na zuwa ne makonni kadan bayan karin girma da kwashinonin ’yan sandan jihohin suka samu karin girma zuwa matsayin Mataimakin Sufeto-Janar.

A kan haka ne ta turo Mohammed Usaini Gumel a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano.

Sauran jihohin da aka tura wa sabbin Kwamishinonin ’Yan Sanda su ne:

  1. ABUJA: Haruna Gabriel Garba.
  2. KADUNA: Garba Musa Yusuf.
  3. ZAMFARA: Garba Ahmed.
  4. SAKKWATO: Hayatu Kaigama Ali.
  5. KATSINA: Aliyu Musa.
  6. YOBE: Mohammed Nuni.
  7. BINUWAI: Julius A. Okoro.
  8. DELTA: Tajudeen A. Abass.
  9. OGUN: Oladimeji Yomi Olarewaju.
  10. ONDO: Taiwo Jesubiyi.
  11. BAYELSA: Romokere Ibiani.

Da yake jawabi bayan sanar da nadin sabbin kwamishinonin, shugaban hukumar aikin dan sanda, Solomon Arase, ya bukace su da su kasance masu sadaukarwa a yayin gudanar da aikinsu.

Arase, wanda tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya ne, ya jaddada cewa aikin ke gaban sabbin kwamishinonin ’yan sandan, musamman a wannan lokaci na sauyin gwamnati yana bukatar kishin kasa da bullo da sabbin dabaru da kuma jajircewa.

Don haka ya umarce su da su gaggauta komawa sabbin wuraren aikinsu su shirya wa aikin da ke gabansa.

Ya kara da cewa hukumar za ta rika sanya ido a kansu domin tabbatar da ganin cewa, su da jami’ansu ba su yi sakaci ko wuce gona da iri wajen gudanar da aikinsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here