Abin da ke janyo dannau yayin barci

0
168

Masana kimiyya na ganin rashin iya motsa jiki bayan farkawa daga barci abu ne da ya daɗe yana faruwa ga bil’adama.

Akwai bayanai daban-daban game da wannan batu na dannau kuma masu bincike a baya-bayan nan sun ce “lamari ne da ba a mayar da hankali a kai ba sosai amma cikin shekara 10 da ta gabata, hankali ya karkata a kai”, in ji Baland Jalal, wani mai nazari game da barci a Jami’ar Havard wanda a 2020 ya kammala abin gwajin farko kan hanyoyin da ake iya magance matsalar bacci ta dannau.

A baya-bayan nan ne kuma aka samu haɗin kai game da yawan mutanen da ke kasancewa cikin wannan yanayi.

Binciken ya kasance ba a lokaci guda ba sannan babu daidaito tsakanin hanyoyin da aka bi wajen gudanar da shi.

A 2011, wani likitan ƙwaƙwalwa Brian Sharpless, wanda a yanzu Farfesa ne a Kwalejin St Mary ta Maryland, ya yi cikakken nazari kan faruwar matsalar a lokacin da yake jami’ar jihar Pennsylvania.

Nazarin da ya yi ya duba bincike 35 da aka yi cikin shekaru hamsin.

A jumulla, binciken ya yi nazarin mutum dubu talatin da shida.

Sharpless ya gano cewa matsalar dannau ta fi faruwa fiye da yadda aka yi tsammani inda kusan kashi 8 cikin 100 na manya ke iƙirarin sun tsinci kansu cikin yanayin a wani lokaci na rayuwarsu.

Adadin ya fi yawa tsakanin ɗaliban jami’a su kashi 28 cikin 100 da kuma masu larurar kwakwalwa su kashi 32 cikin 100.

“A gaskiya ba sabon abu ba ne,” in ji Sharpless wanda kuma yana ɗaya daga cikin marubutan Littafin Dannau: Tarihi da Ƙwaƙwalwa da hangen likitoci.

Bayan fuskantar wannan matsala, wasu suna danganta lamarin ga aljanu ko ma wani lamari da ba a iya bayaninsa.

A zahiri, in ji Jalal, abin da ke janyo matsalar abu ne da ba shi da ɗaukar hankali.

Cikin dare, jikin bil’adama yana kasancewa cikin matakai huɗu na barci.

Mataki na ƙarshe ana kiransa “REM” – lokacin da barci ke nauyi a jikin mutum.

A lokacin ne muke mafarki. A cikin wannan yanayi na nauyin jiki lokacin barci, ƙwaƙwalwar mutum na sagar da jijiyoyin mutum, wataƙila ta hana shi yin wani abu da ka iya cutar da shi.

Amma wani lokacin – kuma masana har yanzu ba su da tabbacin abin da ya sa – ɓangaren da ya fi ko ina kaifi a ƙwaƙwalwar mutum na fitowa ne daga REM.

Shi ne yake sa mutum ya ji shi ya farka. Amma ƙasan ƙwaƙalwarsa na nan a REM in ji Jalal kuma har yanzu yana aike wa da saƙonni ta cikin ƙwaƙwalwa domin gurgunta jijiyoyin.

“Wajen da ya fi kaifi a ƙwaƙwalwa zai fara aiki,” in ji Jalal. “Kana farkawa a ƙwaƙwalwarka amma a zahiri, har yanzu kana jin matsalar barci ta dannau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here