PSG sun ci wasan farko ba tare da Messi ba

0
109

Paris St-Germain ka iya daukar Kofin Ligue 1 idan ta yi nasara a wasa uku nan gaba bayan ta bi Troyes har gida ta doke ta ranar Lahadi.

‘Yan kwallon kungiyar sun mamaye wasan a karawarsu ta farko tun bayan dakatar da kyaftin na Argenitina Lionel Messi.

An dakatar da shi ne sakamakon kai ziyara Saudiyya ba tare da izinin kungiyar ba, ko da yake ya nemi afuwa.

Kylian Mbappe ne ya soma zura kwallo a raga minti takwas da soma wasa sannan Vitinha ya kara ta biyu.

Dan wasan Troyes Xavier Chavalerin ya taimaka wa kungiyarsa ta ci kwallo daya, sai dai Fabian Ruiz ya kara wa PSG kwallo guda inda suka tashi 3-1.

Yanzu PSG tana bukatar maki bakwai ne ta lashe Kofin na Ligue 1 karo na 11.

Tana gaban Lens, wadda ke ta biyu a tebirin gasar, da maki shida ko da yake Lens na da sauran wasa hudu da za ta fafata.

Troyes na mataki na 19 don haka ko kanshin kofin ba ta ji.

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here